
Daga Yasir Ramadan Gwale
Hukumar karbar koke-koken danne hakki da yaki da almundahana da zambar kudade ta jihar Kano ta bankado wata almundahana da zambar kudade da ta shafi wasu daga cikin kananan hukumomin jihar Kano tare da hadin bakin wasu daga cikin shugabannin makarantun primary dake jihar Kano.
Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji ne ya bayyana haka, a lokacin da yake karbar rahoton binciken daga daraktan hukumar da ya jagkranci wannan bincike SA Gusau. Magaji ya bayyana cewa, laifukan da suka bankado sun sabawa dokokin da suka kafa hukumar a shekarar 2008.
Muhuyi magaji ya kara da cewar, hukumarsa ta kwato sama da Naira Miliyan 21 daga hannun wadan da ake zargi da yin almundahanar. A cewarsa wasu daga cikin mutanan da ake zargi sun baiwa hukumar hadinkai wajen gudanar da binciken don gurfanar da wadan da ake zargi da laifukan zambar kudaden.
A wani bayani kuma, da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Maimuna Saidu Bello ta sanyawa hannu, ya bayyana cewar tun kusan a shekarar bara ne, hukumar ta kaddamar da gudanar da binciken akan irin bayanan sirrin da suke samu kan badakalar da ake tafkawa a sashen ilimi na kananan hukumomin jihar Kano. Ta kara da cewar, hukumar ta yi bincike akan mutane sama da 50 wadan da ake zargi suna da hannu dumu dumu cikin almundahanar.