
Daga Abdulrazak Ibrahim
Ƙungiyar kimiyya ta Royal Swedish Academy of Sciences ta baiwa shehunnan malaman kimiyya Rainer Weiss da Barry Barish da Kip Thorne lambar yabo ta Nobel ta kimiyyar makamashi wato Physics, sakamakon gudummawarsu a bincike kan walwalin girabiti (gravity), a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata nan.
Sanarwar ta ƙara da cewa an basu kyautar ne domin binciken “don gudunmawar su akan biciken LIGO da kuma walwalin girabiti”, wato karfin maganadisun dake rike da duniyoyi.
Ita dai LIGO (Laser Interferometer Gravitational-Wave Observatory) wata katafariyar naura ce da ke da fikafikai biyu wanda ko wanne fukafuki ya kai nisan kilo mita hudu. A mahadar wadannan fukafukai a kan harba walkiya mai gudun kilo mita 3,000 cikin mitsitsiyar dakika 7 (7/1000 seconds/0.007 seconds).
Ta saman wannan naura akwai inda takan cafko walwalin girabiti ta kuma auna shi. Wannan bincike ya nuna cewa ƙarfin dake rike da duniyoyi za’a iya gano shi a kuma auna shi ta hanyar amfani da LIGO.
Lambar yabon da wadannan masana suka samu ta hada da kyautar kudi million 9 na Swedish crowns, wanda ya yi daidai da million 400 na naira.