Home Ƙasashen waje Bincike: Yawan Musulmai na ƙaruwa a Ingila

Bincike: Yawan Musulmai na ƙaruwa a Ingila

0
Bincike: Yawan Musulmai na ƙaruwa a Ingila

 

 

Ƙidayar al’umma da aka gudanar a bara ta nuna cewa mutanen da ke bayyana kansu a matsayin Musulmai sun ƙaru daga kashi 4.9% a 2011 zuwa 6.5% a 2021 a Ingila.

BBC ta rawaito cewa bayanin da aka fitar ya ce a lokacin ƙidayar an kuma tambayi mutane game da ƙabila da kuma asalinsu.

Ofishin ƙidaya na ƙasa ne ke gudanar da aikin bayan kowanne shekaru 10.

A ɓangare ɗaya kuma, a karon farko cikin tarihi yawan mabiya addinin Kirista ya yi ƙasa da rabi na jumullar al’ummar Ingila da Wales.

Yawan mabiya addinin Kirista ya yi ƙasa, daga kashi 59.3% a 2011 zuwa 46.2% a 2021.

Baya ga masu bin Addinin Musulunci, wasu da yawansu ya ƙaru shi ne waɗanda ke cewa ba su da addini, inda yanzu suke da kashi 37.2% na yawan al’ummar.