
Za ka iya rage hasken wutar daki a lokacin barci ko kuma a lokacin da ka ke zaune ka ke nazari a can cikin zuciyarka, amma rage hasken wuta na lantarki ko kuma wuta ta fitila a lokacin karatu, ko shakka babu na da matukar illa ga sashen kwakwalwa mai suna Hippocampus da ke kula da harkokin koyo, nazari da kuma tuna abinda aka taba sani ta hanyar karatu ko ji ko gani.
Sabon binciken da aka buga a mujallar Hippocampus ya nuna cewa, ba ma kawai amfani da wutar da ba ta kai ba a lokacin karatu, a’a, daukar lokaci mai tsaho a cikin duhu ko kuma a inda haske ya yi karanci na sauya yanayin tsarin kwakwalwa.
Kwararru akan nazarin kimiyyar lafiyar kwakwalwa ne suka yi wannan bincike, kuma sun yi binciken ne akan wani nau’i na beran daji wanda suka gano cewa nau’i, tsari da kuma fasalin kwakwalwar beran dajin iri daya ne da na dan adam.
An raba wannan nau’i na bera gida biyu, inda aka ajiye wasu daga cikinsu a wadataccen haske na tsawon makonni biyu, daya bangaren kuma aka barsu a yanayi na rashin wadatar haske, suma na makonni biyu.
Bayan fito da su daga wajen ajiyarsu, sai bincike ya nuna cewa berayen da aka ajiye a cikin duhu na makonni biyu sun rasa kaso 30 cikin 100 na Hippocampus dinsu, kuma har sun manta da abubuwa da dama na daga cikin abubuwan da aka horar da su kafin a killace su cikin duhu.
Daga daya bangaren kuma, berayen da aka ajiye a wadatar haske, sai nazari da basirarsu ta kaifafa. Karfin karbar horonsu ya karu haka kuma walwalarsu da kanzar-kanzar dinsu ya karu.
Wani abin al’ajabi shi ne yadda su ma wadancan da aka ajiye a cikin rashin wadatar haske na wani mako biyu suka dawo da kaifin tunaninsu bayan sun samu kimanin wata guda a wadatar haske.
Farfesa Antonio Nunez na jami’ar jihar Michigan ya bayyana cewa, wannan yanayi da berayen da muka ajiye a cikin duhu suka samu kansu ya yi kama da yanayin da mutum ya ke samun kansa a lokacin da ya fito daga kallon fim a sinima, inda ake kashe wuta gaba daya. Wasu za ka samu har manta inda suka ajiye motarsu su ke yi.
Binciken ya nuna cewa, akalla kaso 90 cikin 100 na awanni ashirin da hudunmu na kowace rana, muna kasancewa ne a cikin yanayi na karanci haske (ma’ana dai hasken da bai isa ba). Wannan ko shakka babu yana haifar da abubuwa biyu: Dakushe kaifin kwakwalwa,da kuma hanawa sinadirin protein din da ke taimakawa jijiyoyi watsa sakonni zuwa ga sauran sassan jiki aiki kamar yadda ya kamata.
A saboda haka, a duk lokacin da kwakwalwa ta rasa karsashinta kuma babu sinadaran da za su shaukaka yanayinta, dole ne karfin koyo da nazari zai yi kasa matuka. Ma’ana dai, karacin haske na karanta kaifin kwakwalwa, kamar yadda Dakta Jpel Soler ya bayyana a gudunmawarsa akan wannan batu.
A saboda haka, muke kira ga wadanda ke kashe wuta a lokacin barci kuma suna masu duba wayarsu ta hannu, da ma wadanda ke karatu a gaban wutar da haskenta bai kai ba, da su kauvcewa yin hakan domin dai shi ke haifar da matsalar nan da za ka/ki ji sam ba kya ja.