Home Labarai Ƴan bindiga sun ɗauke dagaci da ɗansa a Bauchi

Ƴan bindiga sun ɗauke dagaci da ɗansa a Bauchi

0
Ƴan bindiga sun ɗauke dagaci da ɗansa a Bauchi

 

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Bauchi ta tabbatar da ɗauke Dagacin ƙauyen Zira, Yahya Abubakar da ɗansa, Habu Saleh a Ƙaramar Hukumar Toro da ke jihar.

Kakakin rundunar, SP Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin a Bauchi.

Ya ce ƴan bindigan sun kai hari ne a ƙauyen da ke ƙarƙashin Caji-ofis na Rishi da ke boda da Jihar Plateau da misalin karfe 2 na dare a ranar Asabar.

Wakil ya ce tuni an tura jami’an bincike na ƴan sanda zuwa jejin da ke yankin.

Ya ƙara da cewa “tuni a ka baza jami’an binciken sirri da sauran jami’an mu na ƴan sanda domin kuɓutar da waɗanda a ka ɗauke.

“A halin da a ke ciki na yanzu, an baza ƴan sanda sun yi wa jejin ƙawanya domin kuɓutar da waɗanda a ka sace.

“Mu na tabbatar wa da al’umma cewa da yardar Allah za mu kuɓutar da su,” in ji shi.