Home Labarai Ƴan bindiga sun ɗauke Kwamishina a Benue

Ƴan bindiga sun ɗauke Kwamishina a Benue

0
Ƴan bindiga sun ɗauke Kwamishina a Benue

Wasu ƴan bindiga sun sace Kwamishinan Gidaje da Raya karkara na jihar Benue, Ekpe Ogbu.

Mai taimaka wa gwamnan jihar kan tsaro, kanar Paul Hemba ne ya tabbatar wa kafar talabijin ta Channels cewar an sace Ogbu da yammacin ranar Lahadi a mahaɗar Adankari kan hanyar Otukpo-Ado.

Ya tabbatar da cewa an gano motar da kwamishinan ke ciki a lokacin sace shi, kuma tuni jami’an tsaro su ka fara bincike.

Sai dai ya ce ba a samu wani labari daga waɗanda su ka sace shi ɗin ba.