Home Labarai Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mai juna-biyu tare da wasu matafiya 5

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mai juna-biyu tare da wasu matafiya 5

0
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mai juna-biyu tare da wasu matafiya 5

 

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya shida shida waɗanda su ka hau motar haya ta Jihar Benue, wanda a ka fi sani da Benue Links a kan hanyar su ta zuwa Jihar Legas.

Jaridar The Punch ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar lokacin da motar ta tashi da ga Gboko da fasinjoji 13, amma sai wasu ƴan bindiga su ka tare ta a daidai Ochaja, kusa da Anyingba a Jihar Kogi da misalin ƙarfe 4 na yamma.

Da ga cikin waɗanda a ka yi garkuwa da su akwai mace mai juna-biyu da wani maraya, inda su ka ce direba ya wuce da sauran fasinjojin guda bakwai.

Direban motar, Emmanuel Owoicho ya shaida wa manema labarai cewa sai da yan bindigar su ka yi musu fashi kafin su tafi da fasinjoji shidan.

Ya ce suna cikin tafiya ne sai hango ƴan bindigar su na fitowa da ga jeji, sai su ka fara harbin iska.

Direban ya ƙara da cewa ya so ya tsere amma sai ya tuna cewa za su buɗe wa motar wuta, shine sai ya tsaya a gefen hanya, inda ya ce sai ya ga wasu da yawa sun fito da ga jeji su ka kuma yi musu fashi.

Ya ce sun musu fashin kuɗaɗe da wayoyi kafin kuma su ka yi awon-gaba da fasinjoji shidan .