Home Labarai Ƴan bindiga sun hallaka sama da mutane 50 a Zamfara

Ƴan bindiga sun hallaka sama da mutane 50 a Zamfara

0
Ƴan bindiga sun hallaka sama da mutane 50 a Zamfara

 

Ƴan bindiga sun hallaka sama da mutane hamsin, har da jami’an tsaro a wani hari da su ka kai kan ƙauyukan Sabon Garin Damri, Damri da kuma Kalahe a Jihar Zamfara.

Premium Times ta rawaito cewa mazauna garuruwan sun tabbatar da cewa sama da mutane 50 ne su ka rasu a harin da a ka yi shi a ranar Juma’a da rana.

Rahoton ya ce jama’a da dama sun ji raunuka kuma an ƙona gidaje da dama.

Ƴan bindigsr sun tsere bayan da a ka ƙaro jami’an tsaro kuma su ka tunkare su.

Jaridar ta ce ba ta samu jin ta bakin Kakakin Rundunar Ƴan Sanda ta Zamfara, Muhammed Shehu ba.