
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da kashe wani dan kasuwa mai suna Biola Osundiya, mai shekaru 40, wanda ke kasuwanci a Legas, Kuma yake zaune da iyalansa a Kwara.
Mai Magana da yawun Rundunar, SP Okasanmi Ajayi, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Ilorin yana mai cewa ‘yan sanda na nan suna bibiyar wadanda suka kashe mutumin.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, ya rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar 20 ga watan Yuli, inda aka yi zargin cewa marigayin ya shiga wata mashaya ne dake tsallaken cibiyar fasaha da raya al’adu ta jihar Kwara inda aka harbe shi a kusa da wajen.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce marigayin na tare da wata yarinya da suke tattaunawa ta wayar tarho lokacin da maharan suka farmake shi.
“Mutane biyu ne suka zo akan babur inda suka harbe shi nan take ya mutu.
Majiyar ta kara da cewa, “Da farko ya kasance a Ilorin din jihar Kwara inda matansa biyu da ‘ya’yansa suke zaune amma kwanan nan ya koma Legas ya fara sana’ar siminti.
Kanin marigayin, Segun, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce lamarin ya jefa ‘yan uwa da abokan arziki cikin rudani.
Ya yi kira ga jami’an tsaro da su kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika domin fuskantar shari’a.