
Ɗan gidan tsohon Mataimakin Sifeto-Janar (mai ritaya) kuma Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Zamfara, Ibrahim Mamman Tsafe.
Daily Trust ta jiyo cewa ɗan gidan Mamman Tsafe, tare da wasu mutane uku, sun rasa rayukansu ne yayin da ƴan bindiga su ka kutsa kai cikin garin Tsafe ɗin a jiya Lahadi da daddare.
A kwanakin nan garin Tsafe na fama da harin ƴan ta’adda, inda su ke kashe mutane da kuma yin garkuwa da wasu domin kuɗin fansa
Ko a watanni biyu da su ka gabata, sai da yan bindiga su ka kashe wani jami’in kwastan da wani mutum ɗaya a garin.