
Kamfanin dillancin labarai na gwamnati, AIB, ya bayar da rahoton cewa, a yau Talata wasu ƴan bindiga suka kutsa kai wajen wani bikin suna tare da kashe mutane takwas a ƙauyen Sandiaba da ke lardin Koulpelogo da ke tsakiyar gabashin kasar Burkina Faso.
AIB ta ruwaito cewa, wasu ƴan bindigan sun kutsa cikin kauyen Sandiaba da ke da nisan kilomita huɗu zuwa Soudoughin a lardin Koulpelogo a jiya Litinin.
Majiyar ta ce maharan sun kutsa kai cikin wani taron suna a cikin iyali, inda suka yi ta harbin kan mai-uwa-da-wabi, har su ka kashe mutane takwas.
A cewar AIB, har yanzu yanayin tsaro na ci gaba da haifar da damuwa a lardin Koulpelogo da ma wasu yankuna da dama a Burkina Faso, duk da matakan da jami’an tsaro ke ɗauka.