Home Labarai Ƴan bindiga sun harbe ɗan takarar jam’iyyar Labour a Imo

Ƴan bindiga sun harbe ɗan takarar jam’iyyar Labour a Imo

0
Ƴan bindiga sun harbe ɗan takarar jam’iyyar Labour a Imo

Wasu ƴan bindiga da ake zargin makasan haya ne sun kashe dan takarar majalisar dokokin Imo na jam’iyyar Labour, LP, Christopher Eleghu.

Kamar yadda rahoton jaridar Punch ya ruwaito, baya ga kashe dan siyasar, ƴan bindigar sun kuma kona gidansa tare da lalata masa kadarori da suka hada da babur.

An tattaro cewa wadanda ake zargin sun kai harin ne da sanyin safiyar Juma’a kuma suka rika harbe-harbe na sama da sa’o’i biyu.

Rahoton ya kara da cewa ‘yan bindigar da sau ka kai harin sun kuma ziyarci gidajen wasu ƴan siyasa a yankin amma kuma ba su same su ba.

Wata majiya da ba ta so a ambaci sunanta ta ce, “Sun kashe Christopher Elehu, wanda aka fi sani da Wasco. Ɗan takarar jam’iyyar Labour a karamar hukumar Onuimo. Sun mamaye gidansa da tsakar dare kuma suka rika harbi har sama da awa biyu.

“Sun kashe mutumin sun kona gidansa. Sun kuma lalata masa dukiya. Da ƴan kauyen nasa su ka fito da safe su samu gawar tasa kwance duk da saran adda a jikinsa.”

Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa game da lamarin na kisan ba.