
Wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan haramtacciyar ƙungiyar IPOB ne, sun kashe wani malamin addinin Muslunci, Ibrahim Iyiorji, a jihar Ebonyi.
An ce sun harbi malamin daf da daf har sau biyu a gaban matarsa a gidansu da ke Isu, a Ƙaramar Hukumar Onicha a ranar Juma’a.
DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa maharan waɗanda ke dauke da muggan makamai, sun kai farmaki gidan malamin akan babura uku da misalin karfe 7 na yamma.
Wata majiya a dangin mamacin ta shaida wa DAILY NIGERIAN cewa an garzaya da shi zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Abakaliki, inda aka yi masa tiyata don cire harsashin da ke jikinsa amma ya rasu a ranar Litinin.
“Shi da matarsa ne kawai suke cikin gidan sai wasu mutane shida sanye da abin rufe fuska, kuma ɗauke da muggan makamai su ka isa gidansu a kan babura uku da misalin karfe 7 na yamma,” in ji wata majiya.
Da ya ke ba da labarin, majiyar ta ce, “suka ɗora bindigar a kan matarsa, suka jawo malamin cikin falo, suka umarce shi da ya kwanta.
“Ya yi biyayya a cikin halin tashin hankali. Sai ɗaya daga cikin maharan ya harbe shi a ciki.
“Yayin da ya yi ihun neman taimako cikin zafi, wani daga cikinsu, ya tambaye shi “au dama ba ka mutu ba?”
“Sai kuma ya sake jan kunamar bindigar, a wannan karon a kafadarsa ta dama; kila ya nufi kirjinsa ne amma bai samu ba.
Majiyar ta kara da cewa, “Sun ƙyale matar sai kuma su ka tsere.”
Tuni dai aka binne malamin a gidansa.
‘Yan sanda ba su yi magana kan lamarin ba har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto.