Home Labarai Ƴan bindiga sun kashe mutane 10 tare da raunata 19 a wajen bikin al’adun Irigwe a Plateau

Ƴan bindiga sun kashe mutane 10 tare da raunata 19 a wajen bikin al’adun Irigwe a Plateau

0
Ƴan bindiga sun kashe mutane 10 tare da raunata 19 a wajen bikin al’adun Irigwe a Plateau

 

Wasu ƴan bindiga sun kashe mutane 10 tare da raunata wasu 19 a wani bikin al’adu da aka yi a unguwar Chando Zerreci da ke Masarautar Irigwe, Ƙaramar Hukumar Bassa a Jihar Plateau.

Lawrence Zango, sakataren yaɗa labarai na ƙasa na Ƙungiyar Matasan Irigwe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a Jos.

Zango ya ce, ƴan bindigan sun kaddamar da harin ne a daren ranar Asabar a lokacin bukukuwan al’ada na ‘Zerreci’ na shekara-shekara, wanda shine bikin su na shiga sabuwar kakar noma.

A cewar Zango, wanda ya yi Allah wadai tare da bayyana lamarin a matsayin “abin takaici da bakin ciki”, waɗanda su ka jikkata a halin yanzu su na karɓar kulawa a asibitin Enos na Miango.

Ya kuma yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da hukumomin tsaro da su samar da dauwamammen mafita kan hare-haren da suke kai wa ga asarar rayuka da dukiyoyi.

Kakakin rundunar ƴan sandan, ASP Ubah Ogaba, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya kara da cewa rundunar ta kai jami’anta dauke da makamai zuwa wurin domin dawo da zaman lafiya.

Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da ma Plateau baki daya da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda, ya kara da cewa jami’an tsaro na bakin kokarinsu wajen tabbatar da tsaron lafiyarsu.