Home Labarai Ƴan bindiga sun kutsa kai wani gida tare da ɗauke ƴaƴa mata biyu a Abuja

Ƴan bindiga sun kutsa kai wani gida tare da ɗauke ƴaƴa mata biyu a Abuja

0
Ƴan bindiga sun kutsa kai wani gida tare da ɗauke ƴaƴa mata biyu a Abuja

Wasu yan bindiga su shida, a ranar Lahadin da ta gabata, sun ɓalla kofar wani gida a unguwar Guita, Chikakore, Kubwa, a karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya, Abuja.

Daily Trust ta jiyo cewa a harin, ƴan ta’addan sun yi awongaba da wasu ƴan mata biyu, yaya da ƙanwa, da ƴar shekara 16 da kuma 14.

Jaridar ta tattaro cewa ƴan bindigar sun tsere ne ta cikin wani jeji, wanda ya hada garin da wani kauye.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin Daily Trust, wani mazaunin garin da ba ya son a buga sunansa saboda tsaro, ya ce tun farko maharan sun dauki wasu yan uwa su uku; ‘yan mata biyu da namiji daya, amma sai suka tafi da ƴan matan biyu, suka sako yaron daga daji.

Majiyar ta ce: “Lokacin da ƴan bindigan suka zo; Ba su yi harbi ba kamar yadda su ka saba, amma sai su ka kutsa kai cikin gidan. Da shigar su, sai mai gidan (wani dan birnin Calabar) ya ruga zuwa ofishin ƴan vigilante, daga nan sai ya garzaya gidan kwamanda kafin kwamandan ya kira wani mutum, tuni yan bindigar sun riga sun tsere,”

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Adeh Josephine ya ci tura.