
Wasu ƴan bindiga sun kai wani hari inda suka kona ofishin ƴan sanda da gidaje uku a ƙauyen Zugu na ƙaramar hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara.
Sai dai wani shugaban matasa a Bukkuyum ya shaida wa jaridar Premium Times cewa babu wanda ya rasa ransa a sanadiyar harin kawo yanzu.
Ya kara da cewa mazauna yankin sun tsere daga kauyukansu zuwa garin Bukkuyum da wasu ƙauyukan da ke cikin ƙaramar hukumar Gummi mai makwabtaka domin neman mafaka daga hare-haren.
BBC Hausa ta rawaito cewa kakakin rundunar ‘yan sanda a Jihar Zamfara Mohammed Shehu, bai amsa kiran da manema labarai suka yi ma sa ba kan harin na ƙauyen Zugu.