
Rahotanni sun ce an yi garkuwa da wasu yara ƴan makaranta da ba a tantance adadinsu ba a karamar hukumar Emure da ke jihar Ekiti, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasa ya ruwaito.
Lamarin dai ya zo ne a daidai lokacin da wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, suka yi yunkurin yin garkuwa da wasu sarakunan gargajiya a Ekiti guda uku amma daga bisani suka kashe biyu daga cikinsu, inda dayan kuma ya tsere.
Gwamna Biodun Oyebanji, yayin da yake tabbatar da sace yaran a yau Talata, ya ci alwashin amfani da duk wata hikima domin bankado wadanda suka aikata laifin da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
NAN ya ruwaito cewa an sace ƙananan yaran ne a makarantar, Apostolic Faith Nursery/Firamare, da ke Emure-Ekiti a yammacin juya Litinin.
Majiyoyin sirri da suka zanta da NAN kan lamarin, sun ce motar bas din da ɗaliban ke ciki ta kasance tana tafiya a kusa da garin Eporo Ekiti lokacin da lamarin ya faru.
Da ya ke magantuwa a kan lamarin, Oyebanji, ta bakin Yinka Oyebode, mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, ya bukaci a kwantar da hankula, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa don ceto yaran.
Ya kuma bukaci ‘yan jihar da kada su karaya kan sace daliban da malamansu, inda ya tabbatar da cewa ana kokarin ganin an ceto su.