Home Labarai Ƴan bindiga sun sace basarake a jihar Kebbi

Ƴan bindiga sun sace basarake a jihar Kebbi

0
Ƴan bindiga sun sace basarake a jihar Kebbi

Ƴan bindiga sun kai wani hari a garin Kanya da ke ƙaramar hukumar Danko-Wassagu ta Jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya inda rahotanni suka bayyana cewa sun yi awon gaba da uban ƙasa na yankin da kuma aƙalla wasu mutane tara.

BBC ta rawaito cewa ƴan bindigar sun kuma kashe mutum ɗaya da kuma raunata wasu mutane uku da yanzu haka ake kula da su a asibiti.

Wannan lamari dai ya wakana ne a daren Asabar zuwa safiyar Lahadi da ta gabata, kamar yadda wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana, wa BBC.

Ya ce : ”Da misalin ƙarfe ɗaya na daren Asabar ɓarayi suka shigo garin Kanya, inda suka kama mutane 10, ciki har da uban ƙasar Kanya, Alhaji isa ɗaya wanda aka kama tare da iyalensa. Sun tafi da mutum 10, sun kashe mutum ɗaya, sa’annan sun jikkata mutum biyu mace da namiji wanda yanzu haka suna kwance a asibiti.”

Mutumin ya bayyana cewa mutanen yankin na zaune cikin halin fargaba da tashin hankali sakamakon jimamin da suke yi na wannan lamari da ya afku.

Ya ƙara da cewa ya zuwa yanzu ba a samu yin magana da waɗanda suka sace mutanen ba, balle ma a fara tunanin yadda za a yi a dawo da su.

Ya ce: ”Ba su tambayi komai ba sun dai shiga gidajen mutane suka tafi da waɗanda suka kama, kuma har yanzu ba a ji daga garesu ba.”

Babban jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansandan jihar Kebbi, ASP Nafi’u Abubakar ya tabbaar da faruwan lamarin inda ya ce a lokacin da rundunar ta sami labarin, jami’anta sun garzaya yankin amma ba su cimma ɓarayin ba.

”Ɓarayin sun ƙetaro ne daga jihar Zamfara, kuma mun sami rahoton cewa sun tafi da mutum tara bayan sun kashe mutum guda a lokacin harin.” In ji shi

ASP Nafi’u Abubakar ya ƙara da cewa wannan harin dai ya zo ne a lokacin da aka kwashe tsawon watanni ba a sami aukuwar irin haka ba a yankin amma a halin yanzu rundunar ta baza jami’anta a sassa daban-daban na yankin domin tabbatar da zaman lafiya.

Jihar Kebbi dai na cikin jihohin arewacin Najeriya da suka daɗe suna fama da matsalar rashin tsaro inda ƴan bindiga ke kai hare-hare akai-akai su kuma sace mutane domin karɓar kudin fansa, amma a baya baya nan hukumomin tsaro sun yi iƙirarin cewa lamarin ya ɗan yi sauƙi sakamakon tsauraran matakai da suka ce suna ɗauka kan ƴan bindigar da suka addabi yankin.