Home Labarai Ƴan bindiga sun sace kwamishiniyar harkokin mata ta Cross River

Ƴan bindiga sun sace kwamishiniyar harkokin mata ta Cross River

0
Ƴan bindiga sun sace kwamishiniyar harkokin mata ta Cross River

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da kwamishiniyar harkokin mata ta Jihar Cross River, Gertrude Njar a jiya Laraba a Calabar.

Wani ganau mai suna Samuel Okon ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa cewa wasu samari da su ka rufe fuska ne su ka fito da kwamishiniyar ta karfi da yaji daga motarta.

A cewar Okon, sun tafi da kwamishiniyar ne a cikin motarsu suka bar motar tata a Calabar ta Kudu.

Kalita Aruku, mai ba Gwamna Ben Ayade shawara kan harkokin yada labarai, ta tabbatar da sace kwamishiniyar a wata hira da NAN ta wayar tarho.

“Eh, majiyoyin tsaro sun sanar da mu cewa an yi garkuwa da kwamishiniyar harkokin mata.

“A yayin da muke magana, jami’an tsaro sun kaddamar da farautar waɗanda su ka yi garkuwar da ita da nufin cafke su tare da kubutar da ita ba tare da wani rauni ba,” inji shi.