
Wasu ‘yan bindiga sun sace mutane da dama lokacin da suke sallar Juma’a a kauyen Zugu na karamar hukumar Gummi.
Kwamishinan tsaron jihar, DIG Maman Tsafe (Rtd), ne ya tabbatar da hakan ga wakilin DW.
Sai dai kwamishinan bai fadi adadin mutanen da ‘yan bindigar suka kwasa ba.
Rahotanni sun ce maharan sun kutsa kai cikin masallacin daidai lokacin da masallata ke jiran sauraran hudubar Juma’a.