Home Labarai Ƴan bindiga sun sace sama da mutane 20 a Kaduna

Ƴan bindiga sun sace sama da mutane 20 a Kaduna

0
Ƴan bindiga sun sace sama da mutane 20 a Kaduna

 

Rundunar ƴan sandan Jihar Kaduna ta baiyana cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutum sama da 20 a unguwar Gimbiya dake Sabon Tasha, Ƙaramar Hukumar Chikun.

Kakakin rundunar ƴan sanda ta jihar, Mohammed Jalige, wanda ya sanar da haka ranar Juma’a a gidan talabijin na ChannelsTV ya ce ƴan bindigan sun farwa unguwar Gimbiya da misalin ƙarfe 1:00 na dare, lokacin da mutane ke kwance suna barci.

Jalige ya ce ƴan bindigan sun shiga unguwar ɗauke da manyan makamai, inda su ka yi kan-mai-uwa-da-wabi, inda a dalilin hakan, mutum biyu su ka rasu.

Ya ce rundunar ta fantsama farautar maharan domin ceto waɗanda a ka yi garkuwa da su.

Wani mazaunin unguwar, Gyara Guga ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da wannan hari, sai dai ya ce ba zai iya tabbatar da adadin yawan mutanen da maharan su ka sace ba.