Home Labarai An binne Sani Ɗangote, ƙani ga Aliko Ɗangote a Kano

An binne Sani Ɗangote, ƙani ga Aliko Ɗangote a Kano

0
An binne Sani Ɗangote, ƙani ga Aliko Ɗangote a Kano
A yau Laraba ne a ka binne marigayi Sani Ɗangote, ƙani ga Aliko Ɗangote, a maƙabartar Alhasawa ta dangin Ɗantata da ke unguwar ƙoƙi a cikin birnin Kano.
Manyan baƙi je dai da su ka haɗa da tawogar Shugaban Ƙasa, gwamnoni, Shugaban Majalisar Dattijai, Ministoci, Sarkin Kano da manya-manyan ƴan kasuwa.
Sauran sun haɗa da tsofaffin gwamnoni da tsohon Shugaban Majalisar Dattijai da sauran manyan baƙi.
Babban Limamin Masallacin Ƙofar Kudu ne ya ja sallar jana’izar a daidai ƙarfe 10:05 na safe a farfajiyar fadar Sarkin Kano.
Marigayin ya rasu ne a wani asibiti a birnin Miami na ƙasar Amurka.
Ya rasu ya bar mahaifiyarsa, matarsa, ƴaƴa da kuma ƴan uwa da dama.