Home Labarai A na sa ran binne Sani Ɗangote yau a Kano

A na sa ran binne Sani Ɗangote yau a Kano

0
A na sa ran binne Sani Ɗangote yau a Kano

 

A yau ne a ke sa ran kawo gawar Sani Ɗangote, ƙani ga Aliko Ɗangote daga Amurka domin a yi masa jana’iza.
A tuna cewa Sani Ɗangote, wanda shi ne mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, ya rasu a Amurka bayan ya sha fama da jinya.
Wata majiya daga dangin marigayin ta sanar da jaridar Daily Trust cewa a na sa ran za a kawo gawar mamacin sannan a yi jana’izar sa a gidan Aliko Ɗangote da ke Nassarawa GRA a birnin Kano.
Marigayin ya bar mahaifiyarsa, matarsa,  ƴaƴa takwas da kuma yaiye da ƙanne.