Home Lafiya Birtaniya ta dakatar da ɗaukar likitoci da ga Nijeriya

Birtaniya ta dakatar da ɗaukar likitoci da ga Nijeriya

0
Birtaniya ta dakatar da ɗaukar likitoci da ga Nijeriya

Gwamnatin Birtaniya ta dakatar da ɗaukan ma’aikatan lafiya daga Nijeriya.

Wannan dai na kunshe ne cikin sabuwar dokar daukan ma’aikatan ketare da Gwamnatin Birtaniyar ta yi wa kwaskwarima da ta wallafa a shafinta na Intanet.

Da wannan dai a yanzu Najeriya ta shiga sahun kasashen duniya da Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana a matsayin masu bukatar gaggawa ta fuskar karancin ma’aikatan lafiya da za su jibinci lamarin kiwon lafiyarsu.

A watan Maris ne WHO ta wallafa sunayen kasashen duniya 55 da ke fama da karancin ma’aikatan lafiya ciki har da Najeriya.

Gwamnatin ta Birtaniya ta ce akwai bukatar Najeriya da sauran kasashen da lamarin ya shafa su mayar da hankali wajen bunkasa harkokin kiwon lafiyarsu musamman ta hanyar dakile daukar ma’aikatan lafiyarsu aiki da ake yi a ketare.

A ranar Alhamis ta makon jiya ce Majalisar Wakilai ta amince da kudirin da ke shirin tilasta wa likitoci share shekaru biyar a Najeriya kafin samun izinin zuwa kasashen waje aiki.

Wani dan Majalisar Wakilan na jam’iyyar APC daga Legas, Ganiyu Johnson, ne ya dauki nauyin kudirin da ke neman a yi wa Dokar Likitoci ta 2004 kwaskwarima.

Galibi ’yan majalisar da suka kada kuri’a baka sun amince da kudirin, sai dai wasunsu sun nemi a yi wa kudirin sakwa-sakwa ta yadda wadanda abin zai shafa za su samu zabin aiki a kasar ko tafiya ketare.

Wannan lamari dai wani sabon abu ne da ka iya kai wa ya zamo sabon rikici a tsakanin Gwamnatin Tarayyar da Kungiyar Likitoci NMA.

Ya zuwa yanzu, akalla likitoci dubu biyu ne ke barin kasar a shekara da sunan ci rani.

Haka kuma, kwarrarun likitocin Najeriya sun yi nisa a kasashen Turai da ’yan uwansu na Gabas ta Tsakiya, inda ke zaman sababbin matattarar likitocin da ke fadin ba dadi cikin kasar a halin yanzu.

Aminiya