
Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya ce gwamnatin tarayya ta dage wajen aiwatar da dokar hana kungiyar malaman jami’o’i, ASUU albashi domin ya zama izina ga sauran kungiyoyin da ka iya shiga yajin aikin nan gaba.
Adamu, wanda ya bayyana hakan a taron tattaunawa na mako-mako da sashin sadarwa na fadar shugaban kasa ya shirya, ya ce ASUU ta dage kan cewa dole ne a biya mambobinta na tsawon lokacin yajin aikin da su ke yi
A cewarsa, dagewar da ASUU ta yi na biyan albashin watanni shida na yajin aikin shi ne ke kawo cikas ga tattaunawar da ake yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyar.
“Idan kun raina kokarin da gwamnati ke yi a jami’a, matakin da gwamnatin ta dauka a yanzu shine ba za ta biya watannin da ba a yi aiki ba.
“Ina ganin wannan shi ne kawai abin da ke hannun gwamnati don tabbatar da cewa akwai hukunci ga wasu halaye irin wannan.