Home Labarai Boko Haram: Sojin Najeriya sun yaye sama da mayaƙa 500 kan sana’o’i da dama

Boko Haram: Sojin Najeriya sun yaye sama da mayaƙa 500 kan sana’o’i da dama

0
Boko Haram: Sojin Najeriya sun yaye sama da mayaƙa 500 kan sana’o’i da dama

 

 

Rundunar sojin Najeriya ta ce nan gaba ne za ta miƙa wasu tsoffin ‘yan Boko Haram sama da 500 da ta yaye, hannun hukumomin farar hula, bayan kammala horon raba su da tsauraran ra’ayi.

BBC Hausa ta rawaitocewa, ɗaruruwan tsoffin ‘yan Boko Haram ne suka yi rantsuwa a ƙarshen mako, tare da kai caffarsu ga gwamnatin Najeriya, da suka yaƙa a baya.

Gwamnatin Najeriya ce ta ɓullo da shirin wanda sojoji ke gudanarwa a 2015, a wani ɓangare na dabarun yaƙi da ta’addanci.

‘Yan Boko Haram waɗanda bisa raɗin kansu suka ajiye makamai kuma suka miƙa wuya ga hukumomin ƙasar ne ke cin gajiyar wannan shiri na musamman ciki har da samun horo kan sana’o’in hannu da sauya musu fahimta kan addini.

An ba su tallafin kyautata tunani da nufin sauke su daga tsattsauran ra’ayi, kafin a mayar da su cikin al’umma.

Babban jami’in kula da shirin mai taken ‘Operation Safe Corridor’, Birgediya Janar Joseph Maina ya ce tun bayan fara gudanar da shi, tsoffin ‘yan Boko Haram 1,070 ne tuni aka mayar cikin jama’a.

Da waɗannan tsoffin ‘yan Boko Haram da aka yaye a ƙarshen mako adadin waɗanda suka ci gajiyar horon ya ƙaru zuwa mutum 1,629.