
Shelkwatar tsaron Najeriya ta ce ya zuwa ranar 16 ga watan Mayu mayakan Boko Haram 53,262 ne suka mika wuya ga hukumomi.
Ta ce mambobin kungiyar 1,627 sun mika wuya tare da iyalansu, ciki har da maza 331 da mata 441 da yara 855 sun mika wuya ga sojoji a yankuna daban-daban tsakanin 1 ga watan Mayu da kuma 14 ga watan.
Daraktan Shelkwatar ta bangaren watsa labarai, Manjo Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan a Abuja.
Ya ce dakarun Najeriya na rundunar hadin kai sun kashe ‘yan ta’adda 43, tare da kama 20 da kuma ceto mutum 63 cikin wadanda aka kama a fadin arewa maso gabahsin kasar cikin mako uku.
Ya ce sun kashe kwamandan Boko Haram Abubakar Sarki a dajin Sambisa a Yuwe da ke karamar hukumar Koduga a jihar Borno.