
Rahotanni daga garin Dapchi da safiyarnan sunce ‘yan kungiyar Boko Haram da suka sace ‘yan matan makarantar Sakandiren Gwamnati a Dapchi din sun dawo da su.
Wani da ya ga lokacin da aka dawo da ‘yan matan, ya shaida mana cewar yaga manyan motoci guda shida suna ajiye ‘yan matan a cikin garin na Dapchi. Sannan kuma,motocin da suka ajiye ‘yan matan sun wuce sun tafi ba tare da an kama su ba.
Zamu kawo cikakken bayani zuwa anjima.