
Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya sauka daga shugabancin jam’iyyarsa ta Conservative a yau Alhamis.
Amma zai ci gaba da kasancewa firaministan kasar har zuwa watan Oktoba.
Za a naɗa sabon shugaban jam’iyyar Conservative a wannan bazarar sannan za a yi sabon firaminista a watan Oktoba ɗin.
Boris Johnson ya gabatar da jawabin yin murabus ɗin nasa a gaban fadar No 10 Dawning Street.
Tun kafin ya kammala yin murabus ɗin a hukumance, har an fara kamfe kan wanda zai gaje shi.
Gabanin yin bayanin murabus din a hukumance an jiyo wani mai magana da yawun fadar Gida Mai Lamba 10 ya ce: “Firaministan zai yi sanarwa ga ƴan ƙasar zuwa an ji ma.”
Mr Johnson ya yi magana ne da Sir Graham Brady, shugaban kwamitin jam’iyyar Conservative na 1922 , inda ya sanar da shi matakin da ya ɗauka, a cewar wata majiya daga fadar No 10.
Majiyar ta ƙara da cewa: “Firaminsita ya yi magana da Graham Brady inda ya amince ya sauka a kan lokaci don ba da damar naɗa wani sabon shugaban a Oktoba.”