
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa, NEMA ta ce a jiya Juma’a ne gobara ta tashi a sansanin ƴan gudun hijira da ke Kalari Muna Elbadawy a Maiduguri, Jihar Borno, inda ta yi sanadiyar mutuwar mutum ɗaya ta kuma raunata mutum 17.
Babban Kakakin NEMA, Yankin Arewa-maso-Gabas, Abdulkadir Ibrahim ne ya sanar da haɗarin a wata tattaunawa da Kamfanin Daillancin Labarai, NAN.
A cewar sa, wajen rumfuna 100 ne su ka lalace kuma mutanen da ke zaune a cikin gidaje sun ɗaiɗaice sakamakon gobarar.
Ya ce gobarar ta fara ne da ga ɗaya da ga cikin rumfunan da misalin ƙarfe 1 na rana lokacin da a ke girki a ciki, inda ya ƙara da cewa an samu nasarar kashe wutar bayan da Jami’an Kwana-kwana na jiha su ka zo.
Ibrahim ya ƙara da cewa tuni dai jami’an NEMA da na ‘Red Cross’ da sauran masu ruwa da tsaki su ka fara kai wa waɗanda abin ya shafa agajin gaggawa.
Ya ce jami’an NEMA da na Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jiha, SEMA su ka je su na auna irin illar da gobarar ta yi.
Sansanin na ɗauke da gidaje 10,00 da kuma mutane 50,000.