Home Labarai Buɗaɗɗiiyar Wasiƙa Zuwa Ga Mai Girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduj

Buɗaɗɗiiyar Wasiƙa Zuwa Ga Mai Girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduj

0
Buɗaɗɗiiyar Wasiƙa Zuwa Ga Mai Girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduj

Bayan gaisuwa mai ɗimbin yawa da fatan alheri, ina fatan gwamna ya dawo daga filin dangwala ƙuri’a daga mazaɓarsa da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa lafiya.

Mai girma gwamna, bayan kammala wani abu mai kamar al’mara da sunan zaɓen ƙananan hukumoni ranar Asabar 11 ga watan Fabrairu, sai mu ka ji kwatsam tsakar daren ranar Lahadi mai girma gwamna ka rantsar da ɗorarrun shugabannin ƙananan hukumomi su arba’in da huɗu. A wajen ramtsuwar ne aka rawaito wai mai girma kana cewa ƙuri’ar da aka dangwala a wannan zaɓen har ya wuce wanda aka dangwalawa Shugaba Buhari a shekarar 2015. Inda mai girma ka ce za ku baiwa Buhari ƙuri’a milyan biyar a zaɓe mai zuwa.
Ya kamata mai girma gwamna ya sani ba’a taɓa yin zaɓen ƙananan hukumomi da ya sami ƙalubale, ƙauracewa da kuma rashin tsari irin wannan a tarihin jihar kano ba. Da farko babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta ƙauracewa zaɓen saboda sun shigar da ƙara kotu domin rashin amincewarsu da tsabagen kuɗin da aka saka musu wajen sayen form. Mutanen gari masu dangwala ƙuri’a kuwa kwanciyarsu suka yi a gida domin babu dalilin fitowa zaɓen da jam’iyya ɗaya ce kawai ta shiga takara. Filin zaɓen kuwa daga ma’aikatan zaɓe sai tarin ƙananan yara waɗanda ba su raina abin kallo. Sai ƴan sanda da sauran jami’an tsaro waɗanda daman an kwaso su daga jihohin maƙobta domin tabbatar da zaman lafiya yayin zaɓen. Akwatunan zaɓe kuwa da sauran kayan aiki ba su fara isowa ba sai wajen karfe biyu na rana wasu wuraren ma sai bayan sallar la’asar. Ƙarshe dai abin da ya faru shi ne jami’an zaɓe da wakilan jam’iyya suka haɗa kai da ƙananan yara suka dangwale ƙuri’un nan tsaf. Haka aka yi a duk faɗin jihar Kano mai kananan hukumomi 44 .

Abin tambaya anan shi ne wai shin a zaben 2019 mai girma gwamnan kana tsammanin haka za a yi zaɓen ne? Shin gwamna yana tsammanin ba za mu fito mu zaɓi jam’iyya ko mutanen da mu ke so a dukkanin madafun iko ba?
Shin mai girma gwamna yana jin zai iya juya zaɓen ƴan majalisar jiha, tarayya, zaɓen gwamna da na shugaban ƙasa?

Lallai Mai girma gwamna ka dauko Dala ba gammo har ka ke yiwa Shugaban ƙasa albishir da ƙuri’a milyan biyar. Shin ka manta ƴan Kwankwasiyya kaɗai a jihar kano sun fi magoya bayanka yawa kuwa? Shin ba don tsoro ba, me ya hana ka barin jagoran kwankwasiyya na ƙasa Dr Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa kano ne? Ya kuma za ka yi da ɗimbin jama’ar da suke goyon bayan jam’iyyar PDP? Shin ina mai girma gwamna zai yi da waɗanda aka zo tashar su suka sauka daga motar Alfa ta goyon bayan shugaba Buhari bayan sun sha baƙar wuya da tarin alƙawurra babu cikawa? Mai girma gwamna ya manta da ɗimbin magoya bayansa da za su bijire masa a wannan karon saboda haraji mara kan gado da ake tsawwalawa mutanen jihar Kano?
Duk waɗannan cincirindon al’umma za su zura ido su bar gwamna ya yi ƴar dangwale kamar yadda suka yi a wannan zaɓen kuwa?

Lallai mai girma gwamna ya san fakewa bayan shugaba Muhammadu Buhari ya ƙare. Ranar zaɓe kowa ta kansa zai yi, ranar nan fa kowa ‘Nafsi-Nafsi’ ya ke yi. Ranar da ko shi Shugaba Muhammadu Buhari bashi da tabbas domin yanzu kan mage ya waye. Babu sauran SAK a zaɓen Najeriya.

A ƙarshe ina fatan mai girma gwamna zai faɗaku cewar kujerar nan ba madauwamiya ba ce kuma akwai wata shari’ar domin za a tambaye mu akan me yasa muka ƙaƙabawa al’umma mutanen da basu zaɓa ba a matsayin masu kula da al’amuransu.

Da fatan za ka huta lafiya.
Wassalamu alaikum

ADO ABDULLAHI