
Wata ƴar kasuwa mai suna Fatima Ismail, a yau Laraba, ta roki kotun shari’a da ke zamanta a Rigasa Kaduna, da ta umarci tsohon saurayinta, Abubakar Shu’aibu da ya biya ta naira 180,000 da ya ranta.
Ismail ta shaida wa kotun cewa ta baiwa Shuaibu rancen kudi naira 230,000 domin ya gyara motarsa kuma ya zuwa yanzu, naira dubu 50 kawai ya iya biyan ta.
Ta ce duk kokarin da ta yi na tsohon saurayin nata ya biya ta kuɗin ta amma ya ƙi biyan ta cikon.
A nasa bangaren, Shuaibu ya ce tsohuwar budurwar tasa ba ta bayyana ko kudin da ta ba shi rance ne ko yauta ba.
“Ba ta son ganina cikin damuwa. Duk lokacin da ta gan ni a wannan hali, sai ta tambaye ni in ba ni kudi sai ta bani,” inji shi.
Ya shaida wa kotu cewa ba shi da aikin yi, inda ya yi alkawarin biyan bashin da Naira dubu ashirin-ashirin duk wata har sai ya kammala biya.
Alkalin kotun, Abubakar Salihu Tureta, ya yanke hukuncin cewa wanda ake kara zai rika biyan N30,000 duk wata daga makon farko na watan Janairun 2023.