Home Labarai Budurwar da ta yi ƙaryar an yi garkuwa da ita a Abuja ta baiwa ƴan ƙasa haƙuri

Budurwar da ta yi ƙaryar an yi garkuwa da ita a Abuja ta baiwa ƴan ƙasa haƙuri

0
Budurwar da ta yi ƙaryar an yi garkuwa da ita a Abuja ta baiwa ƴan ƙasa haƙuri

 

 

 

Amira Sufyan, wata budurwa da ke zaune a Abuja, wacce kwanan nan ta sanar da cewa an yi garkuwa da ita, ta ƙaryata kanta cewa ba sace ta a ka yi ba.

A ranar 14 ga watan Yuni ne dai Amira, a wasu jerin sakonni da ta wallafa a shafinta na Twitter, ta yi ikirarin cewa ƴan bindiga, wanda su ka yi basaja a zuwan ƴan sanda ne su, sun yi garkuwa da ita tare da wasu mutane 16 da aka sace a sassa daban-daban na Abuja, kuma suka tafi da ita cikin wata mota.

Nan da nan rundunar ƴan sandan Abuja ta yi gaggawar tattara jami’anta domin kuɓutar da ita.

DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa Amira ta kai kanta wani asibiti a Legas domin jinya sannan ta bayyana cewa ta kuɓuta ne a hannun masu garkuwa da mutane..

Yayin da har yanzu rundunar ƴan sanda ta Abuja ba ta fitar da sakamakon binciken nata ba, Amira ta shiga shafinta na Twitter inda ta nemi afuwar ‘yan Najeriya kan abin da ta bayyana a matsayin ƙarya.

Da take rubutawa a shafinta na Twitter: @Ameerah_sufyan a yau Litinin, Amira ta ce: “Barka da rana, ina so in nemi afuwar jama’a, ga daukacin sashen ‘yan sanda da abokaina da ‘yan uwana saboda yaudarar su da sakon da ke kasa, ba komai. Babu wani abu irin wannan da ya faru kuma duk kawai ruɗu na ne da tunani mara kyau.

“Ina kuma mika godiyata ga IG da CP Babaji Sunday da suka taimake ni a kan hakan, Allah Ya saka musu da alheri”.

“Ni da gangan na fita daga gidanmu, na je waɗannan wuraren, na shiga daji na hana kaina ci da sha har tsawon kwanaki hudu a haka, babu wani garkuwa da a ka yi da ni, ko kadan. Ina mai bada hakuri da har cikin zuciya ta kuma don Allah a yi min addu’a, ina bukatar ta.