Home Labarai Buhari ya ƙaddamar da kundin tsarin cigaban ƙasa na shekarar 2021 zuwa 2025

Buhari ya ƙaddamar da kundin tsarin cigaban ƙasa na shekarar 2021 zuwa 2025

0
Buhari ya ƙaddamar da kundin tsarin cigaban ƙasa na shekarar 2021 zuwa 2025

 

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da kundin tsarin cigaban ƙasa na shekarar 2021 zuwa 2025 da se maye gurbin tsarin farfaɗo da tattalin arziki, ERGP na shekarar 2017 zuwa 2020.

Kanfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa Buhari ya gabatar da kundin ne kafin a fara taron majalisar zartaswa na yanar gizo a fadar shugaban ƙasa a yau Laraba.

Da ta ke jawabi a yayin ƙaddamarwar, Ministan Kuɗi, Kasafi da kuma Tsare-tsaren ta Ƙasa, Dakta Zainab Ahmed ta ce wannan sabon shirin zai maye gurbin ERPG.

Ta ƙara da cewa ERPG ya taimakawa ƙasar nan wajen fita da ga mashassharar tattalin arziki a 2017 sannan a ka samu bunƙasar tattalin arzikin har sai da ɓullar annobar korona ta zo ta kawo naƙasu.

Ta ƙara da cewa “matsalolin da ake ciki yanzu sun samu ne sakamakon tsare-tsare da ba su dace ba, zurarewar kuɗaɗe da kuma matsalar tattalin arziki da ta shafi duniya baki ɗaya.

“Wannan gwamnatin na ɗaukar matakai masu kwari da za su canja tsarin tattalin arzikin kasar nan da kuma yadda Gwamnati za ta tafiyar da harkokin ta cikin nasara,” in Ahmed.