
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da tashar dakon kaya ta tsandauri, wacce aka fi sani da Dala Inland Dry Port a jihar Kano.
Shugaban ya isa wajen ne da misalin karfe 10:32 na safe, tare da rakiyar wasu daga cikin ministocinsa.
Shugaban ya samu tarbar Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje da Ministan Sufuri, Jaji Sambo da Manajan Daraktan tashar ta Dala inland, Ahmad Rabiu.
Sauran manyan baki da su ka halarci taron sun hada da Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Najeriya, NSC, Emmanuel Jime; Babban Sakatare, Ma’aikatar Sufuri, Magdalene Ajani da tsohon Babban Sakatare, NSC, Hassan Bello.