
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi mi’ara-koma-baya a game da shugabancin jam’iyar APC na riƙo.
Gwamna Nasir El-Rufai ne dai ya ce Buhari ya bada umarnin tsige shugaban riƙo na APC na ƙasa, Gwamna Mai Maka Buni kuma a maye gurbin sa da Gwamna Abubakar Sani Bello.
Sai dai Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta ƙi amince wa da Sani Bello yayin da jam’iyar ke tunkarar babban taron ta na ƙasa a ranar 26 ga watan Maris.
A wata wasika da Buhari ya rubuta wa Shugaban Gwamnonin APC, Gwamna Abubakar Bagudu, ya ce APC na fama da rigingimun cikin gida da ya kamata a magance su kafin babban taron.
A cewar Buhari, akwai Shari’u da dama a kotu da jam’iyar ke fuskanta, inda hakan ka iya sanya wa ta rasa damar sake mulkar ƙasar nan.
A dalilin hakan ne Buhari ya umarci da a ci gaba da tafiyar da jam’iyar a kan ƙadamin da ta ke a da, ma’ana, karkashin shugabancin Buni3, har zuwa lokacin babban taron na ta.