Home Siyasa Zaɓe: Buhari ya bada umarnin tsaurara tsaro a iyakokin Nijeriya — Minista

Zaɓe: Buhari ya bada umarnin tsaurara tsaro a iyakokin Nijeriya — Minista

0
Zaɓe: Buhari ya bada umarnin tsaurara tsaro a iyakokin Nijeriya — Minista

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) da ta tsaurara tsaro a kan iyakokin kasar kafin da kuma bayan babban zaɓe.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a Katsina a jiya Talata yayin da ya ke kaddamar da hedikwatar hukumar ta jihar Katsina.

“Umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar shi ne cewa daga yanzu zuwa lokacin da za mu kammala zabe, dole ne ku tabbatar da tsaron iyakokinmu.

“Dole ne ku tabbatar da cewa iyakokinmu sun samu kariya sosai daga bakin haure da ke son shigowa don haifar da matsala a lokacin zabe, ko kuma shiga zaben ba bisa ka’ida ba.

“Ya kamata hukumarNIS ta yi aiki daidai da umarnin shugaban ƙasa,” in ji shi.

Ministan ya kuma dora musu alhakin tabbatar da sahihancin takardun duk bakin haure.