Home Labarai Buhari bai san ƴan ta’adda sun yi barazanar sace shi ba sai da na faɗa masa — El-Rufai

Buhari bai san ƴan ta’adda sun yi barazanar sace shi ba sai da na faɗa masa — El-Rufai

0
Buhari bai san ƴan ta’adda sun yi barazanar sace shi ba sai da na faɗa masa — El-Rufai

 

 

 

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce shi ne ya shaida wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari game da barazanar da ƴan ta’adda su ka yi na sace shi.

A wani faifan bidiyo da aka fitar a karshen makon da ya gabata, ƴan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasa a watan Maris, sun yi barazanar sace Buhari da El-Rufai.

Ƴan ta’addan sun yi barazanar sace Buhari, bayan da a ka gan su suna yi wa fasinjojin bulala a wani sabon faifan bidiyo.

Daily Trust ta rawaito cewa da yake magana a wani shirin gidan rediyo da Wakilinta ya saurara a daren ranar Laraba, gwamnan ya kuma ce shi da kansa an gargade shi da ya yi hattara har da iyalansa.

Ya ci gaba da bayanin cewa shekaru biyar da suka gabata yana bayar da shawarwarin kai harin bam a sansanonin ‘yan ta’adda a duk inda suke, yana mai cewa ita ce kadai mafita ga matsalar.

“Na kuma ji labarin wani faifan bidiyo inda suka yi barazanar sace Buhari da ni kaina. Ana yawan gargaɗi na da in yi hattara har da iyalana ma. Ta yaya za mu kasance a kasar da ga sojoji, ga ƴan sanda da gwamnatin tarayya amma wasu ƴan ta’adda za su yi barazanar sace shugaban kasa?

“Idan a baya wadanda ke cikin gwamnati suna ganin wannan abin wasa ne kuma suna ganin abin yana faruwa ne a Katsina, Zamfara, Kaduna da Neja, yanzu ga shi nan har kofar gidan mu kuma dole ne mu tashi mu yi maganin wadannan mutane.

“Wannan ne ya sa na gana da shugaban kasa a ranar Lahadi na gaya masa wadannan matsalolin. Ni ma na ba shi labarin bidiyon domin har zuwa wannan rana bai ma san da shi ba. Sai na shaida masa da washegari gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, shi ma ya tabbatar masa da cewa shi ma ya ga bidiyon ne domin ya dauki mataki.

“Shugaban kasa ya tabbatar mani da cewa ya gana da hafsoshin tsaro kwanaki 3-4 kafin ganawar tamu kuma ya ba su umarni karara cewa su gudanar da cikakken aikin soji don tunkarar wadannan mutane. Muna fata, da yardar Allah sojoji da ’yan sandan da aka ba wa umurnin za su gaggauta kammala aikin. Ba sai mun jira sai su (‘yan ta’adda) su kai farmaki kafin mu mayar da martani.

“Dole ne su (sojoji) su bi su duk inda za su yi da su. Maganar gaskiya mun damu da matsalar tsaro amma muna fatan gwamnatin tarayya za ta yi abin da ya dace,” inji shi.