Home Kanun Labarai Buhari da Abdulsalami da Bukola da sauran manyan mutane sun halarci auren ‘yar Dangote

Buhari da Abdulsalami da Bukola da sauran manyan mutane sun halarci auren ‘yar Dangote

0
Buhari da Abdulsalami da Bukola da sauran manyan mutane sun halarci auren ‘yar Dangote

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar juma’a ya ziyarci jihar Kano domin halartar daurin auren ‘yar idan fitaccen attajirin nan dan asalin jihar Kano Alhaji Aliko Dangote, Fatima Dangote, wadda ta angwance da mijinta Jamil Abubakar.

EDaurin auren wanda aka yi shi tsakanin Fatima da Jamil, dan gidan tsohon Sifeton ‘yan sanda na kasa  MD Abubakar, an daura auren da misalinkarfe 112 na rana a fadar mai martaba Sarkin Kano Muhammadu sunusi II.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, Sarki Muhammadu Sunusi na biyu ne ya daura, wanda babban limamin Kano Farfesa Sani Zahradden ne ya jagoranci daurawa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne dai ya kasance waliyyin amarya, ya kuma karbi sadakin Naira 500,000 daga waliyyin Ango.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci wannan daurin aure akwai, tsohon mai baiwa Shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Aliyu Gusau, da tsohon Shugaban kasa Abdulsalami ABubakar da Kakakin majalisar dokoki ta tarayya Yakubu Dogara da Sanatoci da kuma ‘yan majalisar wakilai ta tarayya.

Gwamnoni da ministoci da Sarakunan Gargajiya duk sun samu halartar wannan daurin aure.

Manyan ‘yan kasuwa da attajirai ‘yan siyasa da jakadun kasashen waje duk sun samu damar halartar wannan daurin aure.

Haka kuma, manyan Malamai daga Izala da kuma darika duk sun samu damar halartar wannan daurin aure.

AN tsaurara tsaro sosai a dukkan hanyoyin da suke isa zuwa fadar mai martaba Sarkin Kano, wannan ta sanya ‘yan jaridu basu samu damar kutsa kai wajen dauko rahotanni abin da ya faru wajen daurin auren ba.

NAN