
Sheikh Ahmad Gumi yayi kira da kakkausar murya ga Shugaba Buhari da yayi murabus ba tare da wani bata lokaci ba, domin ya gaza kare rayukan ‘yan Najeriya da ake kashewa a kullum babu kakkautawa.
Malamin yayi wannan kiran ne a masallacin tunawa da Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dake Kaduna, wajen gabatar da Tafsirin Azumi da yake yi duk shekara. Sheikh Gumi ya bayyana cewar a baya lokacin Gwamnatin Jonathan da kashe kashe yayi yawa yayi makamancin irin wannan kiran ga Shugaba Jonatahn da yayi murabus.
Ya kara da cewar, saboda Shugaba Jonathan ya gaza kare rayukan ‘yan Najeriya na yi kira a gareshi da ya sauka ya ajiye aiki, sannan nace kada ya kuma neman tsayawa zabe a kakar zaben 2015 domin kasa sauke nauyin ‘yan Najeriya dake wuyansa. A cewar Sheikh Ahmad gumi.
Ya cigaba da cewar, “kamar yadda na yi magana kan sakacin waccan Gwamnatin ta Jonathan kan batun tsaro haka na yi kiran akan wannan Gwamnatin ta Buhari, wadda sakacinta kan tsaro yafi na Gwamnatin da ta shude ta Jonathan”