
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa wani baturen ƴan sanda (DPO), SP Daniel Itse Amah da ke aiki a Nasarawa da ke jihar Kano, bisa ga bajintar da ya yi ta ƙin karɓar cin hancin Dala dubu 200 dangane da wani bincike da ya ke gudanarwa akan wani zargin fashi da makami.
Buhari ya karrama DPO ɗin ne a wajen taron yaki da cin hanci da rashawar da Hukumar ICPC ta shirya domin tattauna batutuwan da su ka shafi cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikatan gwamnati.
SP Amah ya nuna ƙwarewa da kuma ƙyamar cin hanci lokacin da ya gudanar da aikin sa na kama wani da ake kira Ali Zaki da wasu jami’an ƴan sanda dangane da fashin kudin da ya kai naira miliyan 320.
Kafin wannan lokaci, Sufeto Janar na ƴan sanda, Alkali Baba ya yawaba DPO ɗin saboda abinda ya kira kwarewarsa da jajircewa da kuma nuna bajinta wajen gudanar da aiki.
Da ya ke jawabi a wajen taron, shugaban Hukumar ICPC Farfesa Bolaji Owasanoye ya bukaci haɗin kan jama’a domin ganin an daƙile ayyukan cin hanci a tsakanin al’ummar Nijeriya.