Home Labarai Buhari ya kori shugaban NYSC bayan watanni 6 da naɗa shi

Buhari ya kori shugaban NYSC bayan watanni 6 da naɗa shi

0
Buhari ya kori shugaban NYSC bayan watanni 6 da naɗa shi

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sallami Shugaban Hukumar kula da Matasa Ƴan yi wa ƙasa Hidima, NYSC, Muhammad Kukah Fadah, ƙasa da watanni 6 da naɗa shi.

Kawo yanzu dai babu wani dalili da a ka bayyana cewa shi ne ya sanya Buhari ya sallami Fadah, amma wata nahiyar sirri a fadar shugaban ƙasa ta shaida wa jaridar PRNigeria cewa korar ta sa ba ta rasa nasaba da rashin ƙoƙari tun bayan da ya kama aiki.

Sai dai kuma PRNigeria ta jiyo cewa tuni a ka baiwa Fadah umarnin ya mika ragamar aiki ga ma’aikaci mafi matsayi a hukumar wanda zai zama shugaban na riƙo.