
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga ministan ilimi na ƙasar Malam Adamu Adamu da ya kawo ƙarshen yajin aikin malaman jami’o’in ƙasar.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa shugaban ya bayyana haka ne a ranar Talata inda ya bayar da umarni ga ministan ilimin ƙasar da ya sasanta abubuwan da ake taƙaddama a kai cikin mako biyu sa’annan a kai masa rahoto.
A yau Talata Shugaba Buharin ya tattauna da ma’aikatu da masu ruwa da tsaki waɗanda ke da alaƙa da ɓangaren ilimi a ƙasar da za su iya warware wannan tirka-tirkar.
Shugaban ya kira su ne domin ya samu ƙarin bayani kan dalilin da ya sa wannan yajin aikin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.