
Ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyar SDP, Prince Adebayo Adewole, ya ce idan zai ba da maki a kan aikin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi da jam’iyyar APC, sai dai ya bashi makin F9.
Da ya ke gana wa da manema labarai a Kano gabanin ƙaddamar da yaƙin zaɓen sa, Adewole ya ce gwamnatin Buhari ba ta yi wa talaka wa komai ba banda ma jefa su cikin halin kunci.
Ya ci alwashin magance matsalar tsaro da talauci idan har a ka zaɓe shi a matsayin shugaban kasa a zaɓen watan gobe.
A cewar Adewole, zai samar da masana’antu da gyara da gina sabbin tituna idan ya samu mulkin kasar nan.
Ya kuma yi alkawarin farfaɗo da harkar kasuwanci da masana’antu a jihar Kano, wacce ya siffanta da cibiyar siyasar Nijeriya.