
Gabanin zaben 2023, shugaban kasa na ranar Asabar, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya buƙaci dukkan ƴan takarar a muƙamai daban-daban da su mutunta zaɓin ƴan ƙasa masu kaɗa ƙuri’a, kuma su rungumi sakamakon zaben kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana.
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon( mai ritaya), tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, da tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), suma sun bi sahun Buhari wajen yin kiran.
Buhari, wanda ya yi magana a jiya Laraba a Abuja a wajen rattaba hannu na yarjejeniyar zaman lafiya da jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar shugaban kasa suka yi.
Kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) ne ya shirya, ya kuma bukaci duk wani dan takara da bai gamsu da sakamakon zaben ba da ya garzaya kotu domin bin tsarin shari’ar kasar.
Mambobin kwamitin zaman lafiya na kasa, karkashin jagorancin Janar Abdusalami Abubakar, da shugaba Buhari, da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da Janar Yakubu Gowon, da sauran manyan baki ne suka halarci taron.
Daga cikin ƴan takarar da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar akwai Bola Tinubu na jam’iyyar APC, Peter Obi na jam’iyyar Lebo (LP), Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP, da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da sauransu.