
Shugaban jam’iyyar APC a Jihar Kano, ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau, Ahmadu Haruna Zago, wanda a ka fi sani da Ɗanzago, ya gana da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a daren Asabar.
A tuna cewa tuni dai APC ta dare gida biyu a Kano, inda ta zama ɓangaren gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje da kuma tashin Shekarau.
APC ta shiga rikici ne tun bayan da a ka yi zaɓen shugabannin jam’iya na jiha, wanda ɓangaren Ganduje ya fitar da Abdullahi Abbas, shi kuma tsagin Shekarau ya zaɓi Ɗanzago.
BBC Hausa ta rawaito cewa a ganawar da ya yi da Buhari, shugaban ƙasar ya taya shi murnar a kan zama shugaban jami’ya a Kano.
“Shi [Shugaban kasa] ya tambaye ni ‘me aka samu?’, ni kuma na ce masa ‘an samu shugabancin APC a Kano. Daga nan ne ya taya ni murna’”, a cewar Ahmadu Zago.
BBC ta rawaito Ɗanzago ya ƙara da cewa, ba su tattauna kan rikicin da jam’iyyar ta ke fama da shi a jihar Kano ba, yana mai cewa “tun da batun yana kotu ba mu tattauna a kansa ba. Ka san shugaban kasa ba ya shiga lamarin da ke gaban kotu.”
Bayan da BBC ta tambayi Ɗanzago kan jita-jitar da ke cewa akwai yiwuwar su haɗe da tsohon gwamnan jihar ta Kano, Rabi’u Kwankwaso, Ahmadu Zago ya ce “babu wannan batu. Sai dai ka san ita siyasa babu masoyi ko makiyi na dindindin.”