Home Kanun Labarai Buhari ya aikowa da Gwamnan Kano saƙon godiya – Salihu Tanko Yakasai

Buhari ya aikowa da Gwamnan Kano saƙon godiya – Salihu Tanko Yakasai

0
Buhari ya aikowa da Gwamnan Kano saƙon godiya – Salihu Tanko Yakasai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aikowa da Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR takardar godiya da jinjina bisa irin kyakyawar tarbar da ya samu lokacin da ya kawo ziyarar aiki ta yini biyu a Jihar Kano.
Wasikar dai wadda itace irinta ta farko da Shugaba Buhari ya taba aikawa wani gwamna a jihohin da ya kai ziyara, ta kunshi manyan kalamai masu nuna jindadin sa game da kyakyawar tarbar da ya samu. Yayi amfani da kalmar “stupendous reception” wadda ke nufin irin karba ta ban mamaki da akai masa a yayin ziyarar tashi, da kuma “extraordinary achievements” wato irin gagarumar nasarar da Gwamna Ganduje ya samu wajen kammala aiyuka.
Hakazalika, Shugaba Buhari ya nuna matukar jindadin sa bisa yadda Gwamna Ganduje ya kammala aiyukan gwamnatocin baya da kuma nasa, inda yake nuni da cewa tabbas gwamnati abar dorawa ce, daga inda na baya suka tsaya, batare da sa san zuciya a ciki ba, domin ci gaban al’umma.
Bayan wannan kalamai masu sanyaya zuciya, Shugaba Buhari ya nuna matukar farin cikin sa da wannan irin karramawa da ya samu daga al’ummar mutanen Kano da kuma Gwamnatin Ganduje, wanda wannan ta sa shugaban ya rattaba hannu akan wasu manya manyan aiyukan raya kasa da Kano zata amfana da su. Duk aiyukan nan, su na cikin kadan daga koken da Gwamna Ganduje yayi wa Shugaba Buhari, yayin ziyarar sa Jihar Kano.
Aikin farko da Shugaba Buhari ya sahalewa, shine aikin binne bututun iskar gas daga Ajakuta zuwa birnin Abuja zuwa Kano, wanda zai samar da iskar Gas din da zaa samar da wutar lantarki da ita, don farfado da masana’antu da sauran su, don inganta tattalin arzikin Arewa, musammam ma na Jihar Kano. Wani katafaren aikin kuma, shine na gyaran hanyar Kano zuwa Kaduna zuwa Abuja, wadda kowa ya san irin lalacewa da hanyar nan tayi, kuma Gwamna Ganduje ya koka da wannan a yayi ziyarar Shugaba Buhari, sai gashi kwatsam majalisar zartarwa ta kasa karkashin shugabancin Shugaba Buhari ta amince da yin sabon titi mai inganci daga Kano zuwa Abuja akan kudi naira biliyan dari da hamsin N150Billion, kuma aka baiwa wannan shahararren kamfanin gine-gine na daya a najeriya wato Julius Berger don yin aikin.
Alherin da zuwan Shugaba Buhari ya haifar wa jihar Kano bai tsaya a nan ba, domin kuwa majalisar zartarwa ta sake amincewa da sakin kudi har naira miliyan dari shida N600Million domin yin sabon terminal wato ginin karbar pasinjoji a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, domin inganta harkar sufuri a wannan jiha mai dumbin tarihi.
Akwai wasu alheren da wannan zuwa ya haifar amma saboda kar na cika ku da surutu ya sa na zakulo kadan daga ciki, domin wayarwa da al’umma kai, don sanin irin alheran da Gwamna Ganduje ya samarwa Kano, ta hannun Shugaba Buhari, don ciyar da Kano, da kuma yankin arewa baki daya gaba.
Tabbas Gwamna Ganduje ya ciri tuta, ya kuma zama Sarkin yakin Arewa, bisa yadda ya janyo Shugaba Buhari ya ga gagga-gaggan aiyukan raya kasa da Gwamna ya aiwatar dukda halin ha’ula’i da kasar take ciki na tabarbarewar tattalin arzikin Kasa, amma duk da haka, Gwamna Ganduje aiki aiki aiki kawai yake, ba dare ba rana, yayi na sa, yayi na rago, ya kuma hada da na malalaci, wanda wannan tabbas abun a zo a gani ne.
Ina so nai amfani da wannan dama, wajen kara mika sakon godiya ta ga al’ummar jihar Kano, bisa yadda suke bawa Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR goyon baya, wanda hakan ta sa yake ta aiwatar da aiyukan raya kasa a Kano, kuma duk a cikin kankanin lokaci na shekara biyu. Ina kuma kira da a ci gaba da saka Gwamna Ganduje da Gwannatin sa cikin adduah, domin Allah Ya ba shi ikon ci gaba da aiyukan raya kasa, don ciyar da Kano gaba.