Home Kanun Labarai Buhari ya gargadi Kwankwaso kan sanya sunansa cikin rikicin Siyasar Kano

Buhari ya gargadi Kwankwaso kan sanya sunansa cikin rikicin Siyasar Kano

0
Buhari ya gargadi Kwankwaso kan sanya sunansa cikin rikicin Siyasar Kano
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Fadar Shugaban kasa ta yi gargadi da kakkausar murya akan kokarin jefa sunan Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan rikicin siyasar Kano, dangane da batun cire Shugaban Jam’iyyar APC Haruna Umar Doguwa daga mukaminsa da akai a makon da ya gabata.

Mai magana da yawun Shugaban kasa MalamGarba Shehu ne yayi wannan gargadi a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi yana mai nesanta Shugaba Buhari da abinda su Kwankwaso suke zargin hannunsa akai.

A ranar Asabar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon Gwamnan Kano ya zargi Shugabankasa Muhammadu Buhari da hannu dumu dumu wajen iza wutar rikicin Shugabancin Jam’iyyar APC reshenjihar Kano.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, Shugaban ma’aikatan tsohon Gwamnan, yace Shugaban kasa ne da kansa ya bayar da umarnin a cire Umar Haruna Doguwa daga mukaminsa na Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Kano, duk da cewar shi ne halastaccen Shugaban jam’iyyar.

Garba Shehu yace, wannan zargi da Kwankwaso ya yiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan cire tsohon Shugaban APC na jihar Kano Umar Doguwa ba shi da tushe balle makama.

Babu wani lokac da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taba sanya kansa a cikin wani rikici na shugabancin jam’iyya a wata jha duk Najeriya, dan haka babu wata gaskya a duk zargin da ake yi na hannunsa akan rikicin cikin gida na jam’iyya ajihar Kano ko ma wasu jihohin.

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana da dattakon da ba zai yi kasadar sanya kansa cikin rikicin cikin gida na jam’iyya ya goyi bayan wani bangare ba a ko ina ne a fadin Najeriya, wannan sam bai dace da mutuntakarsa da haiba da muhibba tasa ba”

Ya kara da cewar, a baya an zargi Shugaban kasa, kan rashin sanya kansa cikin rikicin Shugabancin Majalisa domin ya zama ikon majalisar na hannunsa. Domin ya nada wanda yaga dama a matsayin shugabannin majalisar dattawa da ta wakilai.

Garba Shehu yace, abin dariya ne kwarai mutumin da yaki sanya kansa cikin rikicin Shugabancin majalisar kasa wanda yanada iko inda yaga dama, sannan kuma ace sh ne yanzu zai kaskantar da kansa ya sa baki kan shugabancin jam’iyya a jiha, wannan sam ba gaskiya bane kuma ba zai yi gangancin yin hakan ba.

“Ina da yakinin cewar ‘yanKwankwasiyyar da suka zargi hannun Shugaban kasa kan batun cire Shugaban jam’iyyar APC Haruna Doguwa sun yi hakan ne bisa radin kansu, ba tare da umarnin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba”

“Kwankwaso ya san Buhari sosai, kuma shima Shugaba Buhari yasa Kwankwaso sosai, dan haka bana zaton Kwankwaso zai sanya Buhari cikin wannanrikicin cikin gida”

Daga Karshe mai magana da yawun Shugaban kasar ya nemi da ‘yan Kwankwasiyya kada su kuskura su sake sanya Shugaba Buhari kan batun rikicinsu a jihar Kano, yace matsayin Shugaban kasa ya wuce ya kaskantar da kansa ya shiga rikicin shugabancin jam’iyya a wata jiha.

Yace rashn Adalci ne a hari Shugaban kasa Muhammadu Buhari da wannan rikicin na jihar Kano.

NAN