Home Kanun Labarai Buhari ya kai ziyarar bazata Maiduguri

Buhari ya kai ziyarar bazata Maiduguri

0
Buhari ya kai ziyarar bazata Maiduguri

Daga Mustapha Buhari, Maiduguri

A yau Lahadi ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyarar bazata birnin Maiduguri na Jihar Borno don ganawa da dakarun ƙasar da kuma ƙara musu ƙwarin gwiwar murƙushe ‘yan Boko Haram.

A yau ne Najeriyar ke bukin cika shekaru 57 da samun mulkin kai.

A yayin ziyarar, Buhari ya je asibitin da aka kwantar da sojojin da su ka raunana domin duba lafiyar su da gode musu.

Haka zalika ya yanka kek na murnar samun ‘yancin kai a garin Maidugurin, al’amarin da aka saba yi a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya.

Da ya ke jawabi ga dakarun, Shugaba Buhari ya ce: “Ya zama dole jami’an tsaro su jajirce kuma su zama masu kishin kasa don samun zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

Kafin tafiyarsa birnin Maidugurin, shugaban ya yi wa al’umar kasa jawabi akan yadda ya ke tafikar da mulkinsa kuma da irin nasarorin da aka samu.