Home Labarai Buhari ya naɗa yayan mai-ɗakinsa a matsayin shugaban kamfanin buga kuɗi na ƙasa

Buhari ya naɗa yayan mai-ɗakinsa a matsayin shugaban kamfanin buga kuɗi na ƙasa

0
Buhari ya naɗa yayan mai-ɗakinsa a matsayin shugaban kamfanin buga kuɗi na ƙasa

 

 

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Ahmed Halilu a matsayin Manajan-Darakta na kamfanin buga kuɗi na ƙasa, kamar yadda jaridar DAILY NIGERIAN ta jiyo.

Halilu, wanda wan uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ne, ya riƙe kamfanin a matsayin rikon kwarya bayan murabus din Abbas Masanawa a ranar 16 ga watan Mayu.

DAILY NIGERIAN ta jiyo daga majiya mai ƙarfi cewa shugaban ya amince da naɗin ne bisa shawarar gwamnan babban banki na kasa, Godwin Emefiele, wanda ke rike da mukamin shugaban hukumar NSPMC.

Halilu na da kwarewa a harkar banki ta sama da shekaru 23, inda ya yi aiki da African International Bank Limited, AIB da Zenith Bank Plc.

Ya halarci kwas na Manyan Maaikata karo na 39 a 2017 na cibiyar National Institute for Policy & Strategic Studies Kuru, Jos inda ya samu lambar girma ta na National Institute, mni.

Malam Halilu ya yi digirin farko a fannin Noma B. (Agric), Masters in Business Administration da kuma Masters in International Affairs & Diplomacy duk a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.

Har ila yau, mamba ne a Cibiyar Gudanarwa ta Najeriya, NIM.